A rahoton da kafar sadarwa ta Press Tv ta fitar ya tabbatar da samun yariman charles na ingila ya karbai wasu makudan kudade daga iyalan Osama bin Laden bisa wasu dalilai da har yanzu ba’a bayyana ba.
Rahoton ya bayyana yadda wannan labarin ya karade kafafen sadarwa inda mutane da dama ke kallon hakan a matsayin kaskanci mai girma ga yariman na ingila dama masarautar gabadaya.
Wasu daga cikin masu amfani da kafafan sada zumunta kuma na kallon hakan a matsayin ba wani abin mamaki bane domin dama masarautar ta ingila ta shahara da marawa ta’addanci gami da ‘yan ta’adda baya.
Da dama cikin mabiya kafafen na sada zumunta na kallon hakan a matsayin wani mataki ne wanda yariman ya dauka domin bukatun kashin kai amma wasu na ganin wannan dama wani lamari ne da masarautar Ingilan ke goyon baya.
A wallafar sa a kafar tuwita wani mai suna ‘‘Join A Picket Line” ya bayyana cewa ”Sarkin ku na gobe ya karbi euro miliyan daya daga iyalin bin laden. Dan uwan sarkin ku na gobe ya biya yarinyar da ya yima fyade euro miliyan 12 daga cikin kudin ku”
Ko kafin wannan lokaci ma dai an zargin masarautar Ingilan da hada kai da ‘yan ta’adda domin cimma wasu manufofi na siyasa.
A wani labarin na daban shugaban kasar amurka Joe Biden yayi ikirarin kashe Ayman Al-Zawahiri wanda shine ake ganin magajin Osama bin Laden wanda amurkan tayi ikirarin kashe shi a shekarun da suka gabata.
Wannan ikirari na joe biden ya sanya magoya bayan sa sun cika kafafen sada zumunta da babatun yaba masa gami da goga magana ga tsohon shugaban kasar amurkan Donald Trump.
Amurkawa dai na kallon Alzawahiri a matsayin mai mukami lamba ta biyu a kungiyar ta’addanci ta Alqaeda kuma wanda ya tsara harin 11 ga satumba amma bincike ya tabbatar da cewa amurkawan ne kurum ke da wannan ra’ayi.