Biyo Bayan mutuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth, Yarima Charles, ya zama Sarkin Masarautar Ingila, Fadar Mulkin Buckingham ta sanar ranar Alhamis.
Charles mai shekaru 73 ne babban ‘dan Elizabeth. Sauran ‘yayanta sun hada da Gimbiya Anne, 72, Yarima Andrew, 62, da Yarima Edward, 58. Gabanin mutuwarta dukkansu suka garzaya Balmoral don zaman karshe da ita.
A jawabinsa na farko matsayin Sarki, Charles ya sanar da mutuwar mahaifiyarsa da kuma yadda suke jimami.
A wani rahoto na musamman kuma zaku karanta cewa kafin ta bar Duniya, Sarauniya Elizabeth ta biyu, tayi rayuwa da shugabannin kasashen Duniya barkatai.
An yi Firayim Minista 15 a tarihi a yayin da Elizabeth II take mulki, daga Winston Churchill zuwa Liz Truss Kwanaki kadan da hawan Liz Truss sai Sarauniyar ta mutu, ta bar Duniya tana da shekara 96 da haihuwa.
Legit Sky News ta tattaro duka Firayim Ministocin da aka yi wadanda suka hadu da Elizabeth II: 1. Winston Churchill – 1951-55.
Bayan ya sha kashi a zaben 1945, Winston Churchill ya koma kan mulki a 1951, a wannan lokaci Elizabeth ta zama Sarauniya, tana ‘yar shekara 25, shi yana 77.
2. Sir Anthony Eden 1955-57 Firayim Minista Sir Anthony Eden bai dade a gwamnati ba saboda tirka-tirkar siyasa, ya zauna da Sarauniyar a tsawon shekaru kusan uku da ya yi yana shugabanci.
3. Harold Macmillan – 1957-63.
Rikicin siyasa bai kare ba Harold Macmillan ya zama Firayim Minista, Elizabeth II ta dauka ba zai wuce makonni shida a mulki ba, amma ya shafe shekaru shida.
4. Sir Alec Douglas-Home – 1963-64 Tun kafin ya zama Firayim Minista, Sarauniya ta san Alec Lord Home saboda ya tashi ne a gidan sarauta.
Sky News tace alakar ba ta sa Lord Home ya shekara a ofis ba.
5. Harold Wilson – 1964-70 da 1974-76 Harold Wilson ya yi shugabanci na tsawon shekaru sau biyu duk a idon Elizabeth.
Tsohon Firayim Ministan ya rasu a 1995, lokacin Sarauniyar ta shekara 43 a karaga. Firayim Ministocin zamanin Sarauniyar Ingila.
6. Edward Heath – 1970-74 Edward Heath ya yi HotoFirayim Minista a tsakanin wa’adin Harold Wilson a shekarun 1960s da 70s.
7. James Callaghan – 1976-79 Da James Callaghan ya sauka, jam’iyyarsa ta dade ba ta hau mulki ba, Elizabeth II kuwa tana nan.
8. Margaret Thatcher – 1979-90 Duk da Margaret Thatcher tana mace, dangatakarta da Sarauniya bai yi kyawun da ake sa rai ba.
9. John Major – 1990-97 A lokacin mulkin Firayin Ministan ne shi da Elizabeth II suka yi ta fama da yaki a gabas ta tsakiya.
10. Tony Blair – 1997-2007 Har Tony Blair ya yi murabus bayan shekaru goma, sabani iri-iri ya yi ta samu da fadar Birtaniya.
11. Gordon Brown – 2007-10 Elizabeth ta ji dadin mulkin Gordon Brown, a lokacin dangantar gwamnati da fada ta canza sosai.
12. David Cameron – 2010-16 Dama David Cameron ya san Sarauniya ta wajen Yarima Edward, kuma sun hadu ta Sarki William IV.
13. Theresa May – 2016-19 Mace ta biyu da zama Firayim Minista ita ce Theresa May, Sarauniyar ta kan debe mata kewa.
14. Boris Johnson – 2019-22 Da farko kamar ba za ayi shiri ba, amma jaridar tace daga baya Boris Johnson ya zama mutumin ta.
15. Liz Truss – 2022-Yau A makon nan Liz Truss ta samu izinin Elizabeth domin kafa gwamnati, kafin Truss ta gyara zama a ofis, sai Sarauniya mai shekara 96 tayi sallama da Duniya.
Source: LEGITHAUSA