Kungiyoyin bada agaji na duniya sun yi alkawarin taimakawa kasashen yankin Sahel da wadanda ke kewaye da Tafkin Chadi da kudin da ya kai kusan Dala biliyan 2 domin shawo kan yunwar da ta addabi yankunan biyu.
Kasashen yankin da ake saran su ci gajiyar taimakon sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Najeriya wadanda tashe tashen hankula da kuma karancin ruwan sama suka hana aikin noma da samar da abinci.
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace matsalar karancin abincin da ake fama da ita a yankin a shekarar 2019 ya ribanya har sau 4 inda ta shafi mutane sama da miliyan 40 sabanin miliyan kusan 11 da ake da shi shekaru 3 da suka gabata.
Wadannan alkawura sun biyo bayan taron da wata kungiya da ake kira ta Sahel da Afirka ta Yamma ta shirya da taimakon kungiyar kasashen Turai da kuma kungiyar yaki da karancin abinci ta duniya.
A wani labarin na daban kuma Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Amurka Joe Biden, kwana guda bayan da kasar ta kauracewa kada kuri’a kan kudirin dakatar da kasar Rasha daga hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafin da ta yi a Ukraine.
Sa’o’i kadan bayan haka, Afirka ta Kudu na daga cikin kasashe 58 da suka ki kada kuri’a kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya dakatar da Rasha daga kwamitin kare hakkin bil’adama na MDD a matsayin ladabtar da mamayar Ukraine.
Wannan dai shi ne karo na uku da Afirka ta Kudu ke kauracewa kada kuri’a kan kudurorin da aka amince da su kan yakin.
Ramaphosa ya wallafa a shafinsa na twitter a wannan Juma’a cewa ya tattauna da shugaba Biden ta wayar tarho, kuma sun amince amince da bukatar tsagaita bude wuta da tattaunawa tsakanin Ukraine da Rasha.”