Katafaren yankin raya masana’antun fasahohin zamani na Zhongguancun, da ake wa lakabi da “Silicon Valley” na kasar Sin, ya samu karin kaso 27.8 kan kudin shigarasa a watanni 8 na farkon bana, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
A cewar hukumar, kamfanonin bangarorin fasahar sadarwa da laturoni, da fannin injiniya mai nasaba da halittu da sabbin fasahohin kiwon lafiya, sun samu dorewar ci gaba.
Adadin ma’aikata a fannin bincike da kirkire-kirkiren fasaha a kamfanoni dake yankin Zhongguancun, ya kai 751,000 a wancan lokaci, adadin da ya karu da kaso 8.9 akan na makamancin lokacin a bara.
Zhongguancun da aka kafa a shekarar 1988 a arewa maso yammacin birnin Beijing, wanda ya kunshi jami’o’i da cibiyoyin bincike, shi ne yankin raya masana’atun fasahohin zamani na farko a kasar Sin.
A wani labari na daban kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba wajen raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, wanda ke taka rawa wajen inganta sauye-sauyen da take yi na raya bangaren.
Cikin watanni 8 na farkon bana, adadin takardun lamuni da kasar Sin ta bayar a bangaren ya karu da kaso 152 akan na bara, inda ya zarce yuan biliyan 350, adadin da ya dara jimilar wadanda ta bayar a bara baki daya. Takardun lamunin a fanin dakile fitar da sinadarin Carbon kuwa, ya kai yuan biliyan 180 zuwa karshen rubu’in na 2.