Har yanzu ba a iya gano takamaiman shirin da Isra’ila ke da shi kan yankin Gaza da ta mamaye ba bayan kammala yaƙin da take yi. Ko yaya karshen zai kasance?
Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin ya raba maif yawan mazauna yankin dan karami da ke gabar teku da matsugunansu, kuma yunwa na addabar su sakamakon kawanya, a yayin da sanyi ke kara ta’azzara. / Hoto: Reuters
Tun lokacin da Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙi kan Gaza da ta mamaye, shugabannin Isra’ila sun yi kalamai masu karo da juna kan makomar yankin na Falasdinawa bayan an gama yaƙi, inda kowa yake tambayar wanne mataki Tel Aviv za ta dauka.
A ranar 7 ga Nuwamba, Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce “Isra’ila za ta dauki nauyin samar da tsaro a Gaza har iilla ma sha Allah.”
Bayan kwanaki uku, ya sake cewa ƙasarsa ba ta da niyyar ‘mamayar’ ko mulkar Gaza, amma kuma “dole a raba yankin da mayaƙa, masu tsaurin ra’ayi da sake gina shi.”
A ranar 16 ga Disamba kuma, Netanyahu ya sake bayyana cewa, “Ba za ba mu bayar da damar da Fatah za ta maye gurbin Hamas a Gaza ba, wannan kaucewa babbar ƙawarta Amurka ce, wadda ke fatan ganin Fatah ta karɓe iko da Gaza wanda hakan zai bayar da damar samar da kasashe biyu na Falasdinu da Isra’ila.
Masu tsaurin ra’ayi daga ministocin Netanyahu na ci gaba da kira da a sake mamaye Gaza da Hamas, kuma a samar da tsarin da zai kawar da kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinawa gaba daya.
TRT World ta tattauna da ƙwararru guda biyu – tsohon babban jami’in Ma’aikatar Isra’ila, da tsohon jakadan Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinu da aka mamaya – don fahimtar wadanne irin sauyin gudanarwa da siyasa da tsaro za a samu bayan Isra’ila ta kawo ƙarshen yaƙin da take yi a Gaza.
“Isra’ila ba za ta jagoranci Gaza ba” in ji Kobi Michael, wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin darakta janar kuma shugaban sashen kula da harkokin Falasdinu a Ma’aikatar Isra’ila, yayin tattaunawa da TRT World.
Ya bayyana cewa ya kamata a kafa kwamitin amintattu na kasashen Larabawa da suka hada da Masar da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya – tare da wasu Ƙasashen Yamma irin su Ingila da Faransa da Jamus da Amurka, su jagoranci yankin na Gaza.
Michael ya kuma ce “Akwai bukatar kafa sabuwar Gwamnatin Falasdinawa a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da za ta dinga kula da rayuwar Falasdinawa a yankin.”
Ya ci gaba da cewa “Wataƙila, a nan gaba bayan shekaru biyar ko shida wadannan yankuna na Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan za su haɗe waje guda a matsayin siyasa daya da shugabanni guda, ba wai zaman su yanki daya kawai ba.”
Michael, wanda babban mai bincike ne a Cibiyar Nazarin Tsaron Kasa da ke Tel Aviv, ya ce bai ga alamun a nan gaba Isra’ila za ta bayar da damar Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan su hade waje guda ba.”
Idan aka samu haɗewa irin ta siyasa tsakanin Gaza da aka mamaye da Yammacin Gabar Kogin Jordan, to za a iya kafa ‘yantacciyar kasar Isra’ila a nan gaba, amma a yanzu kamata ya yi a mayar da hankali wajen sake kafa shugabancin Falasdinawa.
Hukuncin bai daya
Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ya shiga rana ta 73 – inda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla Falasdinawa 19,435 da suka haɗa da yara ƙanana 7,729, inda sama da mutum 52,286 suka samu raunuka.
Ana fargabar dubban Falasdinawa na kwance a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaƙin ya raba mafi yawan jama’ar Gaza miliyan 2.3 da matsugunansu, kuma yunwa ta jigata yankin da sanyin hunturu ke addaba a yanzu haka.
Yaƙin ya faro ne a yayin da Hamas ta kai wani hari na ba-zata a ranar 7 ga Oktoba kan matsugunai da garuruwan Isra’ila da ke iyakarsu da Gaza.
Hamas ta bayyana cewa sun kai harin ba-zata kan babbar abokiyar adawarsu Isra’ila ne sakamakon yawan harin da ake kai wa Masallacin Ƙudus da rikicin ‘yan kama guri zauna a Yammacin Gabar Kogin Jordan da kuma sake dawo da batun ‘Falasdinu’ kan teburin tattaunawa.
A wani yunƙuri na ɗaga murya, mayaƙan Hamas sun kutsa kai a yankuna da ke da nisan kilomita 22 daga iyakar Gaza, inda suka kashe ‘yan Isra’ila 1,139.
A wasu wuraren, an bayyana cewa sun kashe sojoji 373, inda su kuma dakarun Isra’ila ke ta ƙoƙarin mayar da martani.
Bayan dawowa Gaza, sun kuma kama wasu mutanen 240, da suka hada da jami’an sojin Isra’ila da farar hula.
Daga baya an saki gwamman fursunonin yakin a madadin Falasdinawan da aka ɗaure a gidajen kurkukun Isra’ila wadanda su ma aka sallame su.
Tun wannan lokaci, Isra’ila na ta yin ruwan bama-bamai kan gaza ta sama da ta ruwa da ta ƙasa, inda a yanzu take ƙoƙarin ƙwace iko da iyakokin yankin matuƙar ta yi nasara kan Hamas, wanda mayaƙanta suka kashe sojojin Isra’ila 129 tare da yin ikirarin lalata tankokin yakin Isra’ila da dama.
Kungiyar na kuma riƙe da ‘yan Isra’ila 140 inda suke yawan nuna bidiyonsu don nuna adawa da shiga yankunansu da tankokin yakin Isra’ila suka yi.
A yayin da ake ci gaba da gwabza fada, kwararru na cewa Falasdinawa da suaran kasashen duniya za su kalli duk wani yunƙurin tsaro na Isra’ila a Gaza a matsayin mamayar soji.
- Source: TRTHausa