Daruruwan masu zanga -zanga sun yi tattaki a birnin Tunis na kasar Tunisia yau Asabar don neman janye dakatarwar da shugaban Tunusia Kais sa’id ya yiwa majalisar dokoki kasar a watan Yuli.
Galibin masu zanga-zangar dai magoya bayan jam’iyyar adawa ta Ennahdha ce, mai rinjaye mafi girma a majalisar dokokin Tunusia kafin dakatar da ita da shugaba sa’id yayi.
A ranar 25 ga watan Yuli shugaba Kais Sa’ed ya dakatar da majalisar dokokin Tunisia ta re da cirewa ‘yan majalisar rigar kariya, sannan kuma ya mai da kansa shugaban masu gabatar da kara, bayan da ya zargi jagororin kasar da dama da zama miyagu.
A wani labari na daban asu fafutuka sun ce akwai fargaba a game da batun yanci a Tunisia, a yayin da shugaba Kais Saied ke ci gaba da kama wadanda ake gani abokan hamayya ne, bayan da ya kori gwamnatin kasar tare da dakatar da majalisar dokoki.
‘Yan siyasa da dama da ma ‘yan kasuwa, har ma da alkalai da ‘yan majalisar dokokin da suka rasa kariyar da kundin tsarin mulki ya ba su bayan da Shugaba Saeid ya dakatar da su, sun ce an haramta musu ficewa daga kasar, yayin da aka wa wasu daga cikin su daurin talala, lamarin da ya janyo caccaka daga masu fafutuka.
Matakin mai ban mamaki da Saied ya dauka ya haifar da rashin tabbas a Tunisia, makyankyasar juyin juye hali ta kasashen Larabawa da ya kunno kai shekaru 10 da suka wuce, lamarin da ya assasa tada kayar baya daga masu rajin kare dimokaradiyya a yankin da ya kai ga sauke shugabanni da suka yi mulki da takalmin karfe.
Tunisia, wadda ake jinjina wa a sakamakon nasarar da ta samu wajen tafiyar da mulkin dimokaradiya a gabas ta Tsakiya da ma Arewacin Afrika ta stinci kanta a cikin dabaibayi na rikicin siyasa da matsin tattalin arziki, da kuma annobar Covid -19.