Yan ta’adda sun kashe jandarmomi akalla 13 a wani harin kwanton bauna da suka kai ranar Lahadi a Taparko, wani gari mai filin hakar ma’adinai a arewacin Burkina Faso.
Majiyar ta kuma tabbatar da cewa, baya ga kashe Jami’an Jandarmomin 13, wasu kimanin takwas ko sama da haka sun bace a harin, yayin da wasu takwas din suka jikkata.
Taparko wani gari ne da ake hakar ma’adanai a kai a kai wanda mayakan jihadi suka sha kaiwa hare-hare.
Hare-haren ta’addanci na neman tsananta a Burkina
Harin da ya halaka Jandarmomin Burkina Fason ya zo ne, a daidai lokacin da wasu mutane biyu suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata, lokacin da wata motar bas ta taka nakiya a ranar Lahadi, lamarin da shi ma ya auku. a kusa da garin na Taparko.
A ranar Asabar kuwa mutane 11 ‘yan ta’adda suka kashe a wani hari da suka kai kan wata mahakar zinari a Baliata, da ke arewacin kasar. Wani ganau ya shaida wa AFP cewa wasu mahara 30 ne kan Babura suka kai farmakin.
Burkina Faso dai na fama da hare-haren yan ta’adda masu ikirarin jihadi tun a shekara ta 2015, lokacin da mayakan da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS suka fara kai hare-hare kan iyakokin kasar daga Mali.