‘Yan Siyasa A Sudan Sun Yi Fatali Da Tayin Janar Al-Burhan.
‘Yan siyasa a Sudan sun yi watsi da tayin babban hafsan sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan, na cewa sojoji zasu janye daga tattaunawar yadda za’a magance siyasar kasar.
A sanarwar da kawancen ‘yan siyasan suka fitar da yammacin jiya ‘sun danganta kalamman na Janar Al-Burhan a matsayin wasa da hankali da yaudara.
Suna masu kira ga ‘yan kasar dasu ci gaba da zaman dirshin da suke a Khartoum na neman sojoji su mika mulki ga farar hula.
Shi dai Shugaban soji na Sudan din ya bayyana cewa zai kawo karshen majalisar gwamnatin da ya ke jagoranta, tare da mika mulki ga sabuwar gwamnatin farar hula.
Al-Burhan ya ce sojoji ba za su kara tsoma baki kan batun yadda za a magance rikita-rikitar siyasar da kasar ta Sudan ke ciki ba, za su bar hakan hannun farar hula.
READ MORE : Amurka; Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum 6 Yayin Faretin Ranar ‘Yancin Kai.
An dade ana zanga-zangar kin jinin mulkin soji a Sudan, tun bayan juyin mulkin da sojin suka yi a bara.
READ MORE : AU Ta Yaba Da Samun Ci Gaban Siyasa A Mali Da Guinea.
READ MORE : Falasdinu; Amurka Na Rufa-rufa Akan Kisan Shireen Abu Akleh.