‘Yan sandan Isra’ila sun raunata Falasɗinawa 19 a masallacin Quds.
Hukumar agajin gaggawa ta Falasdinu ta ce an jikkata masu zanga-zanga 19 a hatsaniyar da ta faru tsakaninsu da ‘yan sandan Isra’ila a bakin masallacin Al-aƙsa da ke birnin Quds.
‘Yan sandan Isra’ila sun ce sun shiga harabar masallacin ne domin korar masu zanga-zanga da kuma dawo da doka da oda.
Falasdinawan sun ce ‘yan sandan sun hana su shiga masallacin bayan idar da sallar asuba saboda bai wa Yahudawa damar shiga ziyara.
Wani wanda abin ya faru a kan idansa ya ce “sun rika harba harsashin roba kan masu bautar da ke cikin masallaci”.
READ MORE : Saudiyya ta yi tir da masu kona AlKur’ani.
A ranar Juma’a ma, sai da ‘yan sanda suka jikkata sama da Falasdinawa 150 a rikicin da ya faru a masallacin.
READ MORE : Iraqi Ta Kira Jakadanta A Sweden Bayan Kona Al Kur’ani A Kasar.
READ MOR : Rasha Ta Yi Gargadi Akan Yiyuwar Batakashi Da Kungiyar Tsaro Ta “ Nato” A Yankin “ Artic’.