‘Yan sandan kasar Faransa sun ce akalla mutane sama da 50 aka kama a karshen mako lokacin da magoya bayan kasar Algeria suka gudanar da murnar nasarar da kasar ta samu wajen lashe kofin kwallon kafar kasashen Larabawa, kuma akasarin su an kama su ne kusa da fadar shugaban kasa.
Algeriya ta doke Tunisia da ci 2-0 a wasan karshe da aka kara a Qatar wajen lashe kofin, abinda ya sa magoya bayan kasar a biranen Faransa da suka hada da Paris da Lyon da kuma Roubaix suka fantsama tituna domin nuna murnar su.
Kasa da makonni uku kenan da Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya isa Algeria a wani yunkuri na gyara alakar kasashen biyu bayan sabanin da suka samu a baya-bayan nan wanda ya kai ga musayar janye jakadun juna.
A wani labarin na daban Ofishin mai gabatar da kara na kasar Chile ya bude bincike kan Shugaba Sebastian Pinera kan sayar da kamfanin hakar ma’adinai ta wani kamfani mallakar ‘ya’yansa, wanda ya bayyana a cikin tonon sililin Pandora Papers.
A cewar Marta Herrera, shugaban sashin yaki da cin hanci da rashawa a ofishin mai gabatar da kara na gwamnati, Babban Lauya Jorge Abbott ne ya fara binciken bayan bayanan Pandora sun bayyana sayar da kamfanin hakar ma’adinai na Dominga da wani kamfani “mai alaka da dangin shugaba Pinera,”
Shugaba Pinera dai ya yi watsi da zargin yana mai cewa tuni aka wanke shi daga duk wani laifi a binciken shekarar 2017.
Batun sayar da kamfanin ma’adinan ga ɗaya daga cikin manyan abokan Pinera ya fara ne tun a shekarar 2010, a lokacin shugabancin sa na baya.
Ana iya cewa an samu cigaba na azo a gani iya lashe zaben da sabon shugaban yayi.