Gwamnatin sojin Chadi na karkashin jagorancin Mahamat Idriss Deby Itno, da ga shugaban kasar da ya mutu a sanadiyyar yaki da ‘yan tawayen arewacin kasar a watan Afrilu, bayan ya shafe sama da shekaru 30 yana mulkin kasar.
Deby karami ya sha alwashin gudanar da zabe mai tsafta a kasar, bayan wani shirin sasantawa na watani 18.
Da izinin hukumomin Chadiin aka fito zanga zangar, sai dai masu zanga zanga sun dau wata hanya da ba ta cikin wadanda aka amince su bi.
Shugaban gwamnatin sojan Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana mambobi 93 na sabuwar majalisar rikon kwaryar kasar, watanni biyar bayan ayyana kansa a matsayin shugaba, sakamakon rasuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno.
Akwai dai masu adawa da tsohon shugaba Deby cikin membobin majalisar dokokin rikon kwaryar ta Chadi, sai dai babu mamba ko guda daga cikin kungiyar ‘yan adawa ta Wakit Tamma, ko kuma daga kungiyoyin farar hula da suka yi tir da darewa shugabancin Chadi da karamin Deby ya yi.
Ranar 11 ga watan Mayu, gwamnatin sojin Chadi ta nada tsohon firaministan kasar Albert Pahimi Padacke, kan tsohon mukamin nasa amma na rikon kwarya.
Pahimi Padacke dai shi ne Firaminista na karshe a karkashin tsohon shugaban Chadi marigayi Idriss Deby Itno.