‘Yan Polisario Sun Soke Duk Wata Alaka Ta Tuntuba Da Spain.
‘Yan fafatukar samun ‘yanci na Sahrawi ko Polisario, sun sanar da dakatar da duk wata alaka ta tuntuba da gwamnatin Pedro Sanchez na Spain, bayan da gwammatin Madrid ta goyi bayan matayin Morocco kan yankin na yammacin sahara.
‘Yan Polisarion sun ce sun yi hakan ne domin tilastawa gwamnatin Madris dawowa kan matakin data dauka game da yankin na Saharawi.
Sanarwar da ‘yan Polisarion suka fitar ta ce matakin zai ci gaba har sai lokacin da gwamnmatin ta Pedro Sanchez, ta bi sahun duniya wajen mutunta dokokin kasa da kasa game da hurimin yankin na Saharawi.
A ranar 18 ga watan Maris da ya gabata ne firaministan Spain ya sanar da goyan baya ga matsayin Morocco game da yankin na Saharawi, matakin da bai yi wa ‘yan Polisarion dadi ba.
READ MORE : Iran Ta Kakabawa Amurkawa 24 Takunkumi Bisa Zarginsu Da Keta Dokar Kasar.
Saidai mahukutan Madrid, sun ce kyautata alakarsu da Rabat na da manufar yin aiki tare ne da sanya ido domin yaki da kaurarar bakin haure dake neman shiga turai ba bisa ka’ida ba.
READ MORE : Najeriya; An Kasa Samun Daidaito Tsakanin Gwanoni PDP Kan Batun Karba-Karba.