‘Yan Najeriya a Ukraine na tsaka-mai-wuya.
Wasu dalibai ‘yan Najeriya da suka makale a birni Kherson na Ukraine wanda sojojin Rasha suka yi wa kofar rago na bayyana mwuyacin halin da suka fada bayan mako biyu suna buya a wani dakin karkashin kasa.
Daliban na bukatar kasarsu ta dauki matakin ceto su da gaggawa.
Jerry Kenny ya shaida wa BBC cewa shi da wasu abokansa shida ba su da lafiya saboda mummunan halin da suke rayuwa cikinsa a dakin karkashin kasa kuma ya ce ba su da abinci da sauran abubuwan more rayuwa.
“Wasu cikinmu ma ba sa iya magana saboda fargaba,” inji shi, kuma ya ce gwamnatin Najeriya “ba ta tuntube mu ba da zummar samar mana da ruwa da abinci”.
“Na yi magana da wakilan kasarmu da jakadu da kuma jami’an ma’aikatar harkokin waje kan yadda za a iya kwashe mu daga nan. Amma har yanzu babu labari.”
READ MORE : Majalisar wakilai na binciken bashin tiriliyan 2.6 da gwamnatin Najeriya ke bin kamfanonin mai.
Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya tuntubi jakadun Najeriya da ke Ukraine da Rasha, kuma sun tuntubi takwarorinsu na Rasha da na Indiya domin samar da hanyoyin kwaso daliban daga Ukraine zuwa Najeriya.
Rahotanni na cewa har yanzu akwai daliban nahiyar Afirka fiye da 100, yawancinsu daga Najeriya da ke Kherson.