Yan Majalisar Faransa Sun sanya Hannun Kan Daftarin Kudurin Yin Tir Da Laifin Yakin HKI Kan Falasdinu.
Daftarin kudurin mai taken Kaddamar da tsarin mulkin wariyar launin fata ga Alummar falasdinu, yan majalisar dokokin Faransa 38 ne suka amince da kudurin , wadanda suka wakilci gamayyar sabuwar jam’iyun NUPES ta masu rayin mazan jiya da aka kafa.
Tun bayan da aka kafa HKI a shekara ta 1948 ba bisa Ka’ida ba, ta bullo da wani tsarin na kare Alummar yahudawa da fadada ikonta ayankun nan falasdinawa da ta mamaye domin amfani yahudawan yan share wurin zauna.
Haka zalika ya zo a cikin daftarin kudurin ya bukaci a kakaba takunkumi mai tsauri na sayar mata da makamai, kuma kasar Faransa ta mika daftarin kudurin ga kwamatin tsaro na MDD da zai bukaci rike kadarorin manyan jami’an gwamnati Isra’ila dake da hannun wajen aikata laifukan yaki da nuna wariya launin fata kan falasdinawa.
READ MORE : Sputnik; Taron na Tehran ya nuna gibin dake tsakanin kungiyar tsaro ta NATO.
Nasarar da ta samua a lokacin yaki da ta yai da takarun hadin guiwa na kasashen larbawa a shekara ta 1967 ya kara bata dama fadada manufofinta a gabar yammacin kogin Jodan da zirin Gaza da kuma ikirarin mallakar yankuna da daman a Alummar falasdinau.