Kungiyar ECOWAS ta cire takunkumin da ta dorawa kasar Mali sakamakon juyin mulkin da akayi a watan Agustan bara sakamakon kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula da akayi.
Goita yayi alkawarin mutunta alkawarin da gwamnatin rikon kwaryar kasar tayi na shirin gudanar da zabe domin kafa gwamnatin farar hula a watan Fabarairun shekara mai zuwa, amma shirin zabe na cike da shakku daga kungiyar ECOWAS.
Daya daga cikin masu shirya zanga zangar, Moulaye Yaffa yace suna bukatar baiwa sojojin shekaru 3 domin daidaita al’amura a cikin kasar.a yaki da ‘yan ta’adda.
A wani labarin na daban ma’aikatar tsaron Mali ta tabbatar da kisan da ‘yan bindiga suka yiwa Sojin kasar 5 a wani farmaki kansu jiya Lahadi.
Sanarwar ta bayyana cewa, dakarun suma sun yi nasarar hallaka mayakan ta’addancin 3 tare da kone motar su ko da ya ke suma sojin sun yi asarar motocinsu guda 5.
Sa’o’I kalilan bayan sanarwar Ma’aikatar tsaron ta Mali ita rundunar Majalisar dinkin duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar MINUSMA ta sanar da jikkatar dakarunta 3 wadanda ta ce sun samu rauni ne bayan taka wani abin fashewa gab da sansaninsu da ke Kidal.
Yankin arewa maso gabashin Mali na ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci tun bayan yunkurin mayaka masu ikirarin jihadi a shekarar 2012 da ke neman ‘yancin kansu.
Zuwa yanzu dubunnan fararen hula suka rasa rayukansu galibi mata da kananan yara yayinda dakarun Soji dubunnai suka kwanta dama a yaki da mayakan masu ikirarin jihadi da suka mamaye arewacin kasar.