Yamen Ta Kaiwa Cibiyoyin Kamfanin Mai Na Saudiyya Hare-hare.
Kakakin sojojin kasar Yemen Yahya Saree ya fada a ranar Juma’a cewa, an kai hari da makami mai linzami kan cibiyoyin Aramco da ke birnin Jeddah, kuma jirage marasa matuka sun kai farmaki kan matatun Ras Tanura da Rabigh.
Haka kuma jiragai marasa matuka sun kuma kai hari a cibiyar Aramco a Jizan da Najran, kudu maso yammacin Saudiyya.
Yemen na daukan wadanan hare haren a matsayin maida martani kan yakin da Saudiyya ta shelanta kanta tun cikin watan Maris na shekarar 2015
READ MORE : Kasar Yamen ta kai wa matattar ruwan Saudiyya hari.
Yakin wanda ya shiga cikin shekararsa ta takwas ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da tilastawa milyoyin tsarewa daga muhallansu, bayan jefa kasar cikin hali mafi muni a duniya a cewar MDD.