Yamen; Rayukan Yara 3,182 Suka Salwanta A Cikin Shekaru Takwas.
Wani rahoto da wata cibiya a Yemen, ta fitar ya nuna cewa yara sama da 3,182 ne suka rasa rayukansu a cikin shekaru takwas da aka kwashe ana yaki a kasar.
Rahoton cibiyar dake sanya ido kan al’amuran toye hakkin dan adam, ya kuma ce mata 2,412 ne aka kashe kana wasu 2,825 suka jikkata tun bayan da kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya kaddamar da yaki kan Yemen a watan Maris na 2015.
Rahoton ya kuma koka da yadda cin zarafin mata ya karu da kashi 63 cikin dari a kasar ta Yemen.
A ranar Alhamis MDD, ta sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin dake rikici a kasar Yemen da watanni biyu.
A farkon watan Ramadana ne bangarorin suka cimma yarjejeniyar domin taimakawa ayyukan jin kai a kasar da yaki ya daidaita, saidai an yi ta samun rahotannin keta yarjejeniyar.
READ MORE : Kasashen Musulmi Na Tir Da Kalaman Batancin Da Akayi Wa Annabi Muhammad (saw) A Indiya.
A watan Maris na 2015 ne Saudiyya da kawayenta suka shelanta yaki kan kasar ta Yemen, lamarin da ya jefa kasar cikin hali mafi muni a duniya inji MDD.