Yamen; Kawancen Saudia Sun Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Budewa Juna Wuta.
Sojojin kawancen kasar Saudiya sun keta hurumin yarjejeniyar tsagaita budewa juna wuta tsakaninsu da gwamnatin kasar Yamen har sau 123 a cikin sa’o’ii 24 da sukagabata.
Tashar talabijin ta Al-Masira ta kungiyar Ansarullah ta bada sanarwan cewa kawancen Saudiya sun aike da jiragen sama masu leken asiri zuwa yankuna da damana kasar wadanda suka hada da Ma’arib,Hajjah, Jauf, Saadah,Taiz, Baidaa, Daale da kumakan iyakokin kasashen biyu, wanda haka ya sabawa yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a ranar 02 ga watan Afrilun da ya gabata.
Banda haka labarin ya kara da cewa, sojojin kawance sun kai hare-hare kan sansanin sojojin Yamen a lardunan Hajjah, Ma’arib, Jizaan, Dal’u da kuma Saada.
Kakakin gwamnatin kasar Yamen dai ya bayyana cewa wadannan abubuwan da sukafaru ya nuna cewa saudia ta kawayenta sun karya yarjejeniyar ta 2 ga watan Afrilu.
READ MORE : Falasdinu; Yahudawan Sahyoniyya Sun Kutsa Cikin Masallacin Al-Aksa.
Gwamnatin kasar Saudia da kawayenta sun cilla yaki kan gwamnatin kasar Yamen a ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015 da nufin sake dora Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar bayan da yayi murabus. Amma sun kasa yin hakan, yau shekaru kimani 8.