Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa yanzu yara kanana kimanin miliyan 1 da dubu 400 ne suka tsere daga Ukraine, tun bayan da Rasha ta kaddamar da yakin kan kasar da Rasha ta yi a ranar 24 ga watan Fabarairu.
Kakakin hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF James Elder, ya shaida wa manema labarai a a birnin Geneva cewa, a kowace rana cikin kwanaki 20 da suka wuce a Ukraine, fiye da yara 70,000 ne ke zama ‘yan gudun hijira.
A takaice dai kididdiga ta nuna cewar yaro daya ke zama dan gudun hijira duk bayan dakika 1.
Elder ya kuma jaddada cewa yakin na Rasha da Ukraine na cigaba da kazancewa tare da munanan yanayin da dubban miliyoyin mutane ke rayuwa ta hanyar tagayyara su, tashin hankalin da rabon da a ga irinsa tun yakin duniya na biyu.
A wani labarin na daban Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ya zarta tsohon tauraron kungiyar Arsenal Thierry Henry a matsayin dan wasan da ya fi yawan kwallayen da ya ci a tsakanin ‘yan asalin kasar Faransa.
A jumlace dai Benzema ya ci wa Real Madrid kwallaye 311, 66 a Lyon sai kuma 36 a wasanni 94 da ya buga wa Faransa.
Kwallaye uku wato Hat-trick da Benzema ya jefa a ragar Paris Saint-Germain a gasar cin kofin zakarun Turai a makon da ya gabata, ya bashi damar zarce Alfredo Di Stefano a cikin jerin ‘yan wasan da suka fi zira kwallaye Madrid din a matsayi na 3.