Yakin Ukrain Ya Shafi Farashin Abubuwa Da Dama A Kasar.
Gwamnatin kasar Masar ta bayyana cewa yakin da ake yi a kasar Ukrai ya shafi dukkan banagarorin rayuwa na kasar.
Jaridar Egypt Today ta kasar Masar ta bayyana cewa yakin da kasar Rasha ta fara a kasar Ukrain ya shafi kayakin yau da kullun a kasar daga cikin har da farashin gangan man fetur wanda ya kai dalar Amurka $101.4 a kan ko wace ganga a jiya, da haka kuma zai shafi dukkan kayakin da ake amfani da man fetur farashi.
Banda haka kasar Masar na shigo da alkawa kai tsaye daga kasar Ukrai wanda a halin yanzu ba zai yu ba. Labarin ya kara da cewa tashin farashin makamashi yana tasiri wajen kara farashin dukkan kayaki a kasar. Wani masanin tattalin arziki Hesham El-Shebeini ya bayyanan cewa duk wani rikici da za’a yi a kasashen Rasha da Ukrain Ko Iran Da Iraki ko Amurka da China duk suna taba tattalin arzikin kasar Masar don kasashenwar wadannan kasashe suna hula da kasar Masar ko kasashen yankin sosai.