Rahotanni daga kasar falasdinu na nuni da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanya yahudawan sojojin ta bisa shirin kota-kwana domin aiwatar da ayyukan ta’addanci a kan raunanan falasdinawa sakamakon ayyukan kwatar kai da falasdinawan suka soma.
A jiya talata ne dai a garin Bnei Brak dake gabashin Tel-Aviv wani matukin babur yayi kokarin daukan fansa kan wadansu yahudawan sahayohiyan inda yayi nasarar kashe yahudawa biyar ciki harda dan sanda daya inda a karshe shima ya rasa rayuwar sa sakamakon harin day kai kan yahudawan.
Lamurra sun kara lalacewa ne dai tsakanin falasdinawa da yahudawa ‘yan share wuri zauna a yankunan ”west bank” da kuma gabashin Alquds sakamakon matsantawar yahudawan na haramtacciyar kasar Isra’ila na kwace filaye da gonakin falasdinawa gami da kamu, cin zarafi da kuma sanya takunkuma sakamakon gabatowar wata mai alfarma na ramadana.
Wani lamari da ak tabbatar ya kara harzuka lamurra a yankin na faladinu shine yadda kasashen larabawa suke cigaba da shiryawa gami da dasawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ilan ba tare da lura da halin da larabawa falasdinawa suke ciki ba.
An kashe falasdinawa goma a sakamakon sabbin rikice rikicen da suke faruwa tsakanin bangarorin biyu a baya bayan nan.
Kungiyoyin neman ‘yancin falasdinawa sun yabawa sabon matakin da al’ummar falasdinu suka fara dauka na cire tsoro gami da kokarin kwatar kai daga hannun yahudawa ‘yan share wuri zauna a yankin na falasdinu.
A bangare guda kuma rahotanni sun tabbatar da cewa a ranar talatan firayi minstan haramtacciyar kasar isra’ila Naftali Bennett ya gabatar da wata tattaunawa ta musamman da kwamnadan sojin kasar Benny Gantz da kuma kwamandojin sauran bangarorin tsaro na kasar kuma an sa ran zasu kuma gudanar da tattaunawar ranar larabar nan domin samar da hanyar da zasu cigaba da tabbatar da zaluncin sun kan raunana falasdinawa masu fafutikar neman ‘yancin kasar su.