Yahudawan Iran Na Goyon Bayan Hare-Haren Da Aka Kai Kan Cibiyar Sahyoniya A Arbil.
Wani dan majalisar mai wakiltan yahudawa a majalisar dokokin kasar Iran ya bayyana cewa yahudawan Iran suna goyon bayan hare-haren da dakarun juyin juya halin musulunci na kasar ko IRGC suka kan cibiyar leken asiri na yahudawan sahyoniyya dake garin Arbil na kasar Iraqi
Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Homayun Samen Yah yana fadar haka a safiyar yau Litinin. Ya kuma kara da cewa abinda IRGC ta yi kadanne daga karfin da take da shi. Don a halin yanzun ana gwada karfin sojojin kasar Iran da manya-manyan kasashen duniya.
READ MORE : MDD Ta Yi Tir Da Zartar Da Hukuncin Kisa Da Saudiyya Ta Yi Wa Wasu Mutane 81.
Sameh Yah ya gargadi kasashen da suke makobtaka da kasar Iran kan barin mikyar kasar su yi amfani da kasashensu wajen ayyukan leken asiri da kuma na ta’addanci a cikin kasar Iran.
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran sun wargaza cibiyar leken asiri da kuma horasda yan ta’adda na HKI dake garin Arbil na lradin kurdawan kasare Iraqi a cikin yan kwanakin da suka gabata tare da makamai masu linzami 12. Sun kuma bada rahoton kissan akalla mutane 4.