Shafin arab 48 ya bayar da rahoton cewa, wani adadi mai yawa na yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa kai a yau Litinin a cikin masallacin aqsa tare da keta alfarmar wannan wuri mai daraja.
Yahudawan sun shiga cikin harabar masallacin ta hanyar kofar Magariba, daya daga cikin muhimman kofofin masallacin aqsa.
baya ga haka kuma jami’an tsaron gwamnatin a cikin kayan sarki dauke da bindigogi ne suke ba su kariya domin hana Falastinawa daukar wani mataki na hana yahudawan shiga cikin masallacin.
‘Yan sahyuniya dai suna shiga wannan wuri ne da sunan suna kai ziyara a wani haikal da suke raya cewa na yahudawa ne da annabi Sulaiman ya ajiye a wurin.
Hakan kuma jami’an tsaron Isra’ila sun kame wasu Falastinawa 7 saboda nuna rashin amincewarsu da keta alfarmar wannan wuri mai daraja da yahudawan ‘yan share wuri zauna suke yi.
A wani labarin na daban jaridar Guardian ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, ‘yan sanda sun shiga gudanar da bincike kan sanya wuta da aka yi a kan wani masallaci na musulmi a daren jiya Asabar a garin Manchester.
Rahoton ya ce an sanya wutar ne da dare bayan da musulmi da suke gudanar da harkokinsu a wurin suka bar wurin, inda aka saka wuta da ta yi sanadin jawo gobara a masallacin.
Kafin zuwan jami’an kwana-kwana, wasu daga cikin jama’ar gari da suke wucewa sun fara kawo dauki domin kashe wutar da ke ci a masallacin.
Musulmin da suke tafiyar da lamurran masallacin sun yi godiya ga jama’ar yankin, kan yadda suka nuna damuwa da abin da ya faru da kuma gudunmawar da suka bayar wajen kashe wutar da ke ci a masallacin, lamarin da a cewarsu ya nuna musulmi da al’ummar yankin suna zaune laffiya ne da girmama juna.
A nasu bangaren ‘yan sanda a birnin na Manchester suna ganin cewa harin yana da alaka ne da wasu masu akidar kiyayya da addinin muslunci, kuma sun sha alwashin bin kadun lamarin domin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin su gurfana a gaban kuliya.