Yadda ‘yan Ukraine ke dogon layi domin neman abinci.
Yayin da ake kokarin samar da hanyoyi na jin kai domin fararen hula su fice daga birnin Mariupol ke cin karo da matsaloli, an sami shiga da tallafin abinci da magunguna a birnin da Rashawa ke iko da shi a jiya Laraba.
Fiye da muutum 100 sun yi layi yayin da suke jimirin samun abin da za su ci wanda aka kai cikin wata motar dakon kaya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya sanar.
READ MORE : Rasha Ta Fidda Dalar Amurka A Matsayin Kudaden Sayen Makamashinta.
Wata mata mai ‘ya’ya biyu mai suna Angelina ta ce an ba su biredi da abinci, kuma ta ce ta yi sa’ar isa wurin kafin abincin ya kare. “Ba ko yaushe za ka sani ba… sai kawai ka ji cewa ya kare,” inji ta.
Ta kuma kara da cewa, “ficewa daga nan a motar bas na da matukar wahala a yanzu.”