Sababbin bayanai na fitowa game da yadda tare jirgin kasa a Kaduna da fasa gidan yari da aka yi a Abuja.
Wani a cikin Fasinjojin da yanzu ya samu ‘yanci ya bayyana yadda Boko Haram sun hada-kai da ‘Yan bindiga Da taimakon ‘Yan bindiga aka kai wa jirgin Abuja-Kaduna hari, kuma aka boye fasinjojin cikin jeji.
Wani daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka saki ya bada labarin halin da ya samu kan shi, su ne fasinjojin jirgin kasan da aka tare a hanyar Abuja.
Kamar yadda Daily Trust ta kawo rahoto ranar Litinin, wannan mutum ya ce akwai hadin-kai tsakanin ‘Yan Boko Haram da ‘yan bindigan da suka dauke su.
“Su (Boko Haram) shiga yarjejeniya da ‘yan bindiga domin su amfana da yawan sojojinsu da kuma sanin da suka yi wa jirgin kasan.”
“Har jejin da suka ajiye mu a kusa da Birnin Gwari, ba yankinsu ba ne, sun fada mana sai da suka nemi umarnin ‘yan bindigan yankin.”
Fasinjan da aka dauka Majiyar ta shaidawa jaridar a boye cewa a budadden wuri aka ajiye su, babu komai sai bukkoki uku.
Maza suka raba biyu, mata da yara su ka rabe a cikin guda.
Har da cin nama a jeji “Wasu ranakunan za su yanka mana Saniya. Na karshe shi ne wanda suka yanka domin murnar bikin sallah.”
“Kuma su kan yi mana wa’azi da kan su, ko kuma mu saurari wa’azin wasu fitattun malamai da aka dauka.”
Fasa Gidan yarin Kuje Wannan majiya ta iya tabbatar da cewa wadanda suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja ne suka dura gidan gyaran hali na Kuje a Abuja.
Mutumin da ya kubuta yake cewa ‘yan ta’addan sun yi ta murna a daren da aka fasa kurkukun, wanda a dalilin haka ‘Yan Boko Haram akalla 69 suka sulale.
A wani faifen bidiyo da aka fitar, an tabbatar da cewa ‘Yan kungiyar ISWAP ne suka yi wannan aiki. ‘Yan ta’addan ne ake zargin sun tare jirgin kasa yana tafiya.
An biya N800m Kun ji Daloli da makudan miliyoyi sun yi aiki kafin a saki mutum bakwai cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja da miyagun ‘yan ta’adda suka dauke a watan Maris.
‘Yanuwan Muhammad Paki, Bosede Olurotimi, Abubakar Zubairu, Alhassan Sule, Sadiq Ango, Aliyu Usman sun biya N600m, iyalin Abuzar Afzal sun bada N200m.