Shafin yada labarai na Aljuhainah ya bayar da rahoton yadda aka gudanar da tarukan ranar Idin Ghadir a garin Qatif da ke gabashin kasar Saudiyya.
Wannan taro dai kamar yadda aka sani yana daga cikin muhimman taruka da mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) suke gudanarwa a ko’ina a cikin fadin duniya, domin tunawa da ranar jawabin karshe da manzon Allah (SAW) ya yi bayan kammala aikin hajjin bankwana.
A bisa ruwayoyi da sahabbai 115 suka ruwaito wanda hakan yasa ruwayar ta zama a matsayin tawatur saboda ingancinta,a ranar ne Manzon Allah (SAW) ya bayyana dan uwansa kuma surukinsa kuma sahabinsa Imam Ali (AS) a matsayin majibincin lamarin muminai a bayansa.
Mabiya mazhabar Ahlul bait a kasar Saudiyya wadanda su ne kashi 15 na al’ummar kasar suna gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da wannan rana a yankunan su da suke gabashin kasar, kamar yadda sauran mabiya mazhabar shi’a suke gudanarwa a fadin duniya.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran iqna daga birnin Beirut na kasar Lebanon ya bayar da rahoton cewa, tun a jiya Juma’a ne aka kammala gasar karatun kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin na Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.
Cibiyar kur’ani ta Ulal Qiblatain ce ta dauki nauyin shirya wannan gasa ta karatun kur’ani ta kasa da kasa, wadda aka gudanar ta hanyar hotunan bidiyo kai tsaye a yanar gizo.
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrulla ne dai ke jagorantar lamurran cibiyar ta kur’ani, wadda ta dauki nauyin shirya gasar.
Makaranta kur’ani 322 ne daga kasashen duniya 40 suka shiga gasar, wadda aka fara tun daga ranar 3 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, kuma aka kammala a jiya Juma 16 ga watan na Yuli.
An bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazoa gasar, inda Usama Abdullah karbala’i daga Iraki ya zo na daya, sai kuma Muhammad ali Kasim daga Lebanon ya zo na biyu, yayin da Majid Ananpour daga kasar Iran ya zo na uku.