Yadda talauci ke tursasa iyaye a Sri Lanka zaɓen wanda za su sa makaranta a cikin ƴaƴansu
Malki mai shekara 10 na cike da farin cikin da ba za ta iya ci gaba da barci a gado ba.
Ta riga ‘yan uwanta biyu mata, da biyu maza tashi da awa ɗaya saboda ta kankare farcenta.
Yau ce ranar da za ta koma makaranta kuma so take ta yi fes.
Sai dai kuma dole ne ‘yan uwanta su ci gaba da zama a gida – ita kaɗai iyayenta za su iya ɗaukar nauyi.
Wata shida da suka gabata, Sri Lankda ta shiga halin karyewar tattalin arziki mafi muni tun bayan samun ‘yancin kanta.
Duk da cewa an ɗan samu natsuwa a ƙasar da ke kan tsibiri, har yanzu iyalai na ɗanɗana hauhawar farashi da kuma rashin ayyukan yi ga matasa.
Ɗar-ɗar ɗin da iyaye ki ciki
Sai mahaifiyar Malki mai suna Priyanthika ta dakatar da yaran nata, sai sun sayar da itace kafin su tafi makaranta.
Farashin kayan abinci ya yi tashi mafi girma a tarihi, inda ya kai kashi 95 cikin 100.
Wasu lokutan babu wanda yake samun abincin da zai ci a gidan su Malki.
Duk da cewa ba a biyan kuɗin makaranta a Sri Lanka, ba a bayar da abinci a makarantun.
Idan aka ƙara da kuɗin kayan makaranta da na mota, Priyanthika ba za ta iya ɗaukar nauyin su ba.
Ta ce tana buƙatar rupee 400 (dala 1.09) duk rana don biya wa kowannensu kuɗin makarantar.
Cikin hawaye, ta ce: “A da duk yaran nan suna zuwa makaranta, ba ni da kuɗin tura su yanzu.”
Malki za ta koma makarantar ne saboda takalmanta da kayan makarantar ba su lalace ba.
Amma kuma ‘yar uwarta Dulanjalee na can kan gado tana kuka, tana baƙin cikin rashin komawa makarantar a yau.
“‘Yar leleta ki daina kuka,” mahaifiyarta na rarrashinta. “Zan ƙoƙarta na kai ki gobe.”
Harkokin ilimin da aka yi wa illa
Yayin da gari ya waye, yaran da za su je makaranta na zarya a kan tituna cikin fararen kaya, a bayan babura ko kuma cike a motocin a-kori-kura.
Prakrama Weerasinghe ne shugaban makarantar Kotahena Central Secondary College kuma a gabansa ake wannan faman a kullum.
“A ranakun makaranta, idan muna taron safe yara kan suma saboda yunwa,” a cewar sa.
Gwamnati ta ce ta fara raba shinkafa a makarantu, amma makarantu da yawa sun faɗa wa BBC cewa ba su karɓi wani tallafi ba.
Mista Weerasinghe ya ce ɗalibai sun rage zuwa makarantu da kashi 40%, kafin daga baya a tilasta masa roƙar malamai su fara zuwa da abinci domin bai wa ɗalibai.
Joseph Stalin ne babban sakatare na ƙungiyar Ceylon Teachers Union. Ya ce da gangan gwamnati ta ƙi lura da yawan iyalan da suke cire yaransu daga makarantun saboda tsadar rayuwa.
“Gwamnati ba ta damu da kawo ƙarshen matsalar ba. Asusun yara na UNICEF da wasu shirye-shiryen na daban sun gano tare da bayyana matsalar fiye da gwamnatin Sri Lanka,” in ji shi.
UNICEF ta ce abin zai yi wa mutane wuya wajen ciyar da kansu a watanni masu zuwa, yayin da hauhawar farashin ke ci gaba da ƙaruwa.
Fata na ƙarshe?
Yayin da gwmnati ta gaza shawo kan matsalar, ƙungiyoyin agaji sun yunƙuro domin shiga tsakani.
Samata Sarana, gidauniya ce da ke tallafa wa mabuƙata a birnin Colombo tsawon shekara 30.
A yanzu, ɗakin ajiyar abincinsu na cike da ɗalibai mayunwata a faɗin birnin.
Yayin da ƙungiyoyin ke tallafa wa yara 200 a rana, a bayyane take suna fama wajen taimaka wa yaran baki ɗayan su.
“Sun ba mu abinci, da motocin hawa, sun ba mu komai da za mu iya yin karatu,” a cewar Manoj mai shekara biyar lokacin da yake kan layi tare da abokansa.
Bayan Malki ta koma gida daga makarantar a ranar farko, ta bai wa mahaifiyarta labarin irin ɗaɗin da ta ji da ta ga ƙawayenta.
Amma ta faɗa mata cewa tana buƙatar sabon littafi, sannan ta ce malamai sun ce a ƙaro kuɗin sayen kayan aiki a makarantar.
“Idan muka samu abincin da za mu ci ma a yau, sai mu yi maganar yadda za a samu na gobe,” in ji Priyanthika.
“Wannan ce rayuwarmu.”