Kamar yadda binciken kwakwaf ya tabbatar ubadar tattakin tunawa da waqi’ar karbala na bana wanda ake gudanarwa a kasar Iraki kuma ke samun mzaiyarta masu musharaka a wannan tattaki daga sassa daban daban na duniya, sai dai kash yadda binciken mu ya tabbatar a kwai yiwuwar wannan shekarar za’a samu babban gibi a lamarin gudanar da wannan daddadiyar ibada da aka jima ana gudnarwa.
Tattakin arba’in dai na zaman taro mafi tara jama’a a fadin duniya a wannan lokaci kuma a kan samu masu musharaka a wannan babbar ibada daga addinai da fahimtoci mabambanta, kama daga musulmi, kirista, sa’annan shi’a da sunnah duk sukan shiga wannan tattaki mai dinbin tarihi.
Binciken mu ya tabbatar da cewa zaiyi wahalar gaske a gudanar tattakin na bana kamar yadda aka saba a shekarun baya domin tun fara gabatowar ranakun tattakin an fara samun sabbin dokoki daga gwamnatocin kasashe inda suke nuna cewa duk wanda ba’ayi masa allurar rigakafin korona ba to ba za’a bashi dama domin yin musharaka a wannan babbar ibada ta tattaki ba.
Binciken namu dai ya kuma tabbatar da yadda da dama cikin mutane masu sha’awar musharaka a tattakin na arba’in sakamakon an tsorata su da farfagandar hadarin kamuwa da cutar ta annobar korona suna shirin fasa kudurin su na shiga sahun mazaiyartan na wannan shekara.
Tattakin zuwa yanzu ya zama daga dag cikin wasu tarukan addini wadanda suka samu gindin zama a tsakanin musulmi musamman masoya iyalan gidan annabta wadanda ke da akidoji daban daban kama daga mabiya mazhabar shi’a dama mabiya mazhabar ahlu sunnah.
Asalin falsafar tattakin arba’in baya rasa nasaba da nuna soyayya ga jikan manzon Allah Imam Hussain (A.S) wanda aka kashe a filin karbala a shekara ta 61 bayan hijira.
Ana sa ran dai za’a gudanar da ibadar tattakin bana amma sai dai ana tsoron samun tasgwaro sakamakon annaobar cutar ta korona mai wuyar sha’ani.