Kamar yadda kafar yada labarai ta ”raidforums” ta sanar ya tabbatar da cewa an samu wasu sun iya kutse cikin manhajar da aka dorawa kula da zaben ‘yan majalisar Iraki.
Kamfanin ”DarkMatter” dai mallakin kasar hadaddiyar daular larabawa (Dubai) shine aka bama aikin lura gami da tattara rahotannin zaben ‘yan majalisar wanda aka gudanar a kasar Iraki, kuma bincikrn kwakwaf din da kamfanin ”raidforums” suka gabatar ya tabbatar da cewa an iya yin kutse a manhajar kamfanin ”DarkmMatter” kuma an samu bayanan irakawa masu kada kuri’a a kalla miliyan tara da rabi.
Kamfanin ”DarkMatters” wanda mallakin kasar Dubai ne shine dai kuma ke da alhakin tabbatar da tsaro gami da amincin zaben ta hanyar yanar gizo gizo, hakan yake tabbatar da yadda kamfanin yayi kasa a gwuiwa wajen gudanar da aikin sa ko kuma an hada baki dashi domin aiwatar da rashin gaskiya a zaben na majalisar Iraki.
Rahotanni suna tabbatarwa kasar Dubai tana da ikon canja sakamakon zaben na Iraki domin kamfanin da aka dorawa aljakin kula da zaben mallakin ta ne, amma sai dai dukkan alamu suna tabbatar da cewa wannan rukunin wadannan masu kutsen a zaben na Iraki yahudawan Isra’ila ne.
Wannan shine lambar telegram ta mai kula da shafin telegram na ”raidforums” wadanda sukayi wannan bincike, (+972568988640, @arielsapir).
Wadanda suke gabatar a wannan bincike sun tabbatar da cewa wannan kutse da akayi a manhajar zaben Iraki zai bada damar a iya fitar da sakamakon masu zabe miliyan tara da rabi da magudi, ma’ana ana iya fitar da kowanne sakamako daya daga cikin miliyan tara da rabin can a matsayin sakmakon biyu ko fiye da hakan.
Kutsen haramtacciyar kasar Isra’ila a zaben Iraki ya sanya shakku gami da lalacewar abubuwa, sa’annan ya sanya rashin amincewa da sakamakon zaban na majalisar Iraki, kamar yadda masu bincike suka bayyana.
Ko a kwanakin baya ma dai tsohon wakilin ingila a NATO a wani wallafa da yayi mai taken ”NATO’S sweet dream on the shores of caspian sea” ya bayyana yadda haramtacciyar kasar Isra’ila tayi kutse kuma ta haddasa yakin daya gabata tsakanin kasashen azarbeijan da kuma Armenia wanda hakan yake nuna yadda haramtacciyar kasar Isra’ila ke ta kokarin samar da hargitsi a kasashen yankin gabas ta tsakiya kuma ta hanyoyi mabambanta.