Ya Kamata A Warware Rikicin Ukrain Ta Hanyar Tattaunawa.
A ranar laraba da ta gabata ce shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya sanar a hukumance aniyarsa ta kaddamar da harin soji a kasar Ukrani, yace basu da wani zabi da ya rage banda su kaddamar da harin soji a kasar Ukrain domin su kawo karshen tsoma baki da sojojin Ukrain ke yi a harkokin yankuna biyu dake Gabashin kasar da suke sanar da ballewa daga Ukrain , kuma ya siffata fadada ayyukan Nato a gabashin yankin a matsayin babbar barazana
Kakakin kwamitin tsaro na majlisar shawara ta kasar Iran Mahmoud Abbaszadeh y ace kungiyar tsaro ta nato ta kange rasha ta kusancin iyakokinta don haka muna shawartar Nato da ta san ina ne iyakokinta.
Yace matakin da rasha ta dauka mayar da martani ne domin Nato ta sabama kundin tsarin mulkinta kan kungiyar tsaro ta nato, kuma ta kara fadada karfinta har ma ta kusanto kan iyakokin Jamhuriyar Musulunci amma ta fuskanci mayar da martani da ya dace
Daga karshe ya nuna cewa akwai wasu muhimman abubuwa guda biyu game da UKrain na farko yana da kyau a warware rikcin ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, na biyu kuma batun hakkin dan Adam wanda yake da hatsari sosai, domin iran ta damu sosai game da hakkokin yan kasar mata da yara kanana.