Yaƙi ya jefa mutum 100,000 cikin mawuyacin hali a Mariupol – Ukraine.
Ma’aikatar tsaro ta Amurka, Pentagon, ta ce sojojin Ukraine na yin nasarar sake karbe iko ta kasa daga mamayar sojojin Rasha, musamman a garuruwa da biranen da ke kudancin kasar.
Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin dakarun Rasha da na Ukraine a birnin Mariupol mai tashar jirgin ruwa, birnin da Rasha ta zafafa yi wa ruwan wuta da makaman roka da na Atilare.
A sakon bidiyo na baya-bayan nan, Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce halin da ake ciki a Mariupol ya munana.
READ MORE : Zan ƙirƙiri ‘yan sandan jihohi idan na zama shugban ƙasa – Aminu Tambuwal.
“Akwai kusan mutum 100,000 a birnin da ke cikin mawuyacin hali saboda an toshe su baki daya. Sama da mako ɗaya ban da ruwan bama-bamai babu abin da ake yi musu, babu abinci, babu ruwan sha, babu magani, suna cikin tashin hankali.” in ji shi.