A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasika ga taron kawancen kare al’adun da aka gada daga kaka da kakani na Asiya.
Xi Jinping ya jaddada cewa, kafuwar kawancen kare al’adun da aka gada daga kaka da kakani na Asiya, za ta taimaka ga kare al’adun gado na Asiya, da kuma karfafa cudanya a tsakanin nau’o’in wayewar kai daban daban na Asiya, tare da sa kaimin ci gaban wayewar kan dan Adam.
Ya ce kasar Sin na son hada kai da sauran kasashen Asiya, wajen inganta mu’amala a tsakaninsu, ta fuskar fasahohin kare al’adun gado, a karkashin laimar kawancen su, tare da samar da dandali na yin shawarwari a tsakanin wayewar kai mabambanta na duniya, don inganta fahimtar juna, da kaunar juna a tsakanin al’ummun kasashe daban daban, da tabbatar da ganin ci gaban wayewar kan dan Adam baki daya.
An dai bude taron ne a birnin Xi’an, hedkwatar lardin Shaanxi na kasar Sin. (Lubabatu Lei)