Tauraron finafinan Hollywood da ke Amurka Will Smith ya lashe kyautar gwarzon jarumi na bana da yafi kowa nuna bajinta a matsayin acta, saboda rawar da ya taka a matsayin mahaifin fitattun ‘yan wasan tennis na duniya Venus da Serena Williams a wani sabom fim da King Richard.
Sai dai Will Smith ya yi abin ba za ta a wajen bikin, inda ya je ya shararawa mai gabatar da shirye shirye Chris Rock mari saboda abinda ya kira shaguben da ya yiwa iyalin sa.
Will Smith ya yi nasara ne da film dinsa mai suna Coda, wanda ya karkata ga barkwanci, wanda ke matsayin karon farko da jarumin ya lashe irin wannan kyauta duk da rawar ganinsa a manya fina-finai da suka fito da sunansa irinsu Bad Boys da Independence Day da kuma Men In Black cikin fiye da shekaru 30 da ya shafe a masana’antar.
Daga cikin wadanda suka lashe lambar girma a wajen bikin da akayi a birnin Los Angeles akwai Jane Campion a matsayin Daraktan da yafi fice da Jessica Chastain a matsayin tauraruwar da tafi fice, sai kuma Troy Kotsur a matsayin mai taimakawa tauraro.
A wani labarin na daban Fim din Nomadland da ke nuna yanayin rayuwar tsofaffin Amurkawa masu gararamba a cikin kwarababbiyar motar akori-kura, ya lashe lambar yabo ta Oscar saboda kyawun daukar hotonsa.
Kazalika ta zama mace ta biyu a tarihi da ta lashe kyautar a matsayinta ta mai bada umarni bayan Kathryn Bigelow wadda ta fara bude babin irin wannan tarihin a shekaarr 2010, lokacin da aka karrama ta saboda fim din “The Hurt Locker.”
Zhao ‘yar asalin China ce, amma kafafen yada labarai na kasarta ba su yada labarin nasararta ba.
A can baya, Zhao ta taba janyo cece-kuce a China saboda yadda ta caccaki kasarta a wata hira da ta yi da manema labarai.
A bangare guda, Frances McDormand ita ma ta samu lambar yabo ta gwarzuwar jaruma, yayin da Anthony Hopkins ya lashe kyautar a matsayinsa na gwarzon jarumi.
Hopkins mai shekaru 83, ya zama jarumin fina-finai mafi tsufa a tarihi da ya lashe kyautar ta Oscar.