Kwararrun hukumar Lafiya ta Duniya WHO kan sha’anin rigakafi sun amincewa mutane da ke da garkuwa jiki mai rauni su karbi rigakafin covid-19 fiye da sau 2 na dukkanin nau’ikan alluran da ake amfani da su a yanzu.
WHO da ke tsokaci kan matakin bayan tun farko Amurka ta shiga sahun farko wajen baiwa al’ummar ta rigakafin a karo na 3 sabanin 2 da hukumar ta sahale, ta ce mutane da dama na bukatar karin allurar rigakafin a karo na 3 don samun cikakkiyar kariya daga cutar.
Kudirin Majalisar Dinkin Duniya na ganin ta yiwa kashi 10 na al’ummar kowacce kasa rigakafin cutar kafin karshen watan Satumban da ya gabata ya gamu da cikasa saboda karancin alluran rigakafin a kasashe 56 ko da ya ke kasha 90 na manyan kasashe sun cimma kudirin.
Hukumar ta WHO ta koka da yadda har yanzu kaso mai yaw ana kasashen Duniya ke fama da kamfar allurar duk da fatan da ake da shin a ganin fiye da kasha 2 bisa 3 na al’ummar Duniya sun karbi rigakafin kafin karshen shekara.
Acewar hukumar ta na duba yiwuwar bayar da damar yiwa mutane allurar a karo na 3 la’akari da karancin alluran a wasau kasashe musamman na matalauta.
Sashen kwararrun kan sha’anin rigakafi a hukumar wanda ake kira da SAGE zai sake nazarin batun tare da fitar da matsaya a ranar 11 ga watan Nuwamba.