Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gabatar da wani shiri a yau laraba, wanda ta ce a karkashin sa za ta shawo kan cutar sankarau nan da shekarar 2030, ta hanyar rage yawan mutane akalla dubu 250,000 da cutar ke kashewa a duk shekara.
Shugaban hukumar lafiyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce lokaci ya yi da za a shawo kan cutar sankarau a duniya baki daya ta hanyar hanzarta fadada amfani da kayan aikin da ake da su da suka hada da alluran rigakafi, jagorantar sabon bincike da karfafan binciken ganowa da magance dalilai daban -daban da suke haddasa cutar, sai kuma baiwa wadanda cutar ta sankarau ta shafa kulawa ta musamman.
Sankarau dai cuta ce da ke haddasa kumburi a ganuwar da ta kewaye kwakwalwar dan adam da kashin baya, galibi sanadiyyar kamuwa da kwayoyin cuta, lamarin da kan sanya ta zama annoba mai saurin yaduwa.
Binciken kwararru ya nuna cewar Sankarau na kashe akalla mutum daya daga cikin 10 da suka kamu da ita, galibinsu yara da matasa, yayin da take barin Hakanan akalla mutum 1 daga cikin biyar tare da nakasa tsawon lokaci, kamar farfadiya, raguwar karfin ji da gani, maatsalar jijiyoyi da akuma raunin kwakwalwa
A cikin shekaru 10 da suka gabata, annobar Sankarau ta fi yaduwa ne a kasashe 26 da ke yankin kudu Saharar Afirka Senegal zuwa Habasha.
A wani labarin na daban hukumomin kiwon lahiya a kasar Cote D’Ivoire ta kaddamar da yiwa yara da yawan su ya kai dubu 90 da suke da shekara daya zuwa 4 alurar rigakafi da kamuwa da cutar sankarau.Cutar dake ci gaba da yiwa yara da dama ila a kasar kamar dai yadda wani rahoto daga hukumar lahiya ta kasar ta tabbatar.