WHO; Mafi Yawancin Alummar Duniya Na Shakar Gurbatacciyar Iska.
Kididdigar baya bayan nan da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar ta nuna cewa kusan kaso 99 cikin dari na Alummar Duniya suna shakar Gurbatacciyar Iska ne , inda ta koka game da rashin tsafatatacciyar iska da take haddasa mutuwar miliyoyin mutane a duk shekara.
Ana ta bangaren babbar darektar hukumar kula da lafiya da canjin yanayi Maria Neira ta fadi cewa kusan kashi 100 na alummar duniya suna shakar iska da ta sabama ma’auni da hukumar lafiya ta amince da shi, sai dai matsalar tafi kamari a kasashen mafi talauci a duniya.
Idan ana iya tunawa a shekarar da ta gabata ma majalisar dinkin duniya ta fadi cewa duk da takaita yawan tafiye –tafiye da sanya dokar takaita zirga –zirga sun taimaka wajen inganta yanayin Iska amma har yanzu dai ita ce babbar matsala da take ci wa duniya tuwo a kwarya.
READ MORE : Har yanzu Ba’a san Makomar Fasinjoji 168 Ba Bayan Mako Daya Da Kai Harin Jirgin Kasa A Najeriya.
Ana sa bangaren shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhnom Ghebreyesus yace damuwar da ake da shi na hauhawar farashin makamashi da ya samo asali sakamakon harin da Rasha ta kai a Ukrain, amma dole ne a yi aiki tare wajen kawo canji a cikin lamarin.