Arewacin Gaza na ci gaba da fuskantar yunwa da buƙatar kayan agaji mai yawa, da karin hasashen samun damar shiga da kuma ci gaba da kokarin samun karin taimako iri-iri a yankin, in ji mataimakin babban daraktan hukumar samar da abinci ta MDD (WFP) Carl Skau.
Kasashe 18 sun yi kira ga Hamas da ta saki wadanda take garkuwa da su domin tsagaita wuta
Shugabannin kasashe 18 da ake ci gaba da garkuwa da ‘yan kasarsu a Gaza da aka yi wa ƙawanya, sun buƙaci a sake su cikin gaggawa tare da cewa hakan zai kai ga abin da suka kira “sahihancin kawo karshen tashin hankali.”
Sanarwar da shugabannin kasashen Ajantina da Austria da Brazil da Bulgaria da Canada da Colombia da Denmark da Faransa da Jamus da Hungary da Poland da Portugal da Romania da Serbia da Spain da Thailand da Birtaniya da kuma Amurka suka fitar ta ce makomar wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza, “wadanda ke da kariya a karkashin dokokin kasa da kasa, abin damuwa ne sosai da al’ummar duniya.”
“Muna jaddada cewa yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da take kan teburin tattaunawa, za ta sa a tsagaita wuta a Zirin Gaza, lamarin da zai sauƙaƙa ƙarin taimakon jinƙai da za a kai a duk fadin Gaza, da kuma kai ga kawo karshen tashin hankali,” ya ce.
Hamas ta matsa wa Isra’ila lamba da ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza idan tana so ta saki mutanen da take garkuwa da su.
DUBA NAN: Zulum Ya Amince Da Fitar Da Kudi Domin Tallafawa Ɗalibai
Hamas ta sake jaddada bukatar Isra’ila ta kawo ƙarshen yaƙin Gaza a matsayin wani bangare na duk wata yarjejeniya ta sako mutanen da aka yi garkuwa da su a can, kamar yadda Sami Abu Zuhri, wani babban jami’i a kungiyar ta gwagwarmayar Falasdinu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, yana mai cewa matsin lambar da Amurka ke yi wa Hamas ba shi da wani amfani.