Rahoton ya ce, tun daga lokacin haihuwarta, Neda tana fama da matsalar shanyewar wani bangaren jiki, amma kuma duk da haka mahaifanta suna koyar da ita karatun kur’ani, kafin daga bisani mahaifinta ya fara kai ta makarantar kur’ani.
A cikin irin wannan yanayi ta iya koyon karatun kur’ani da kuma hardace surori masu yawa, inda a halin yanzu ta hardace izihi kusan ashirin a kanta.
Neda tana daga cikin yara masu wata hazaka ta musamman wadanda babban malamin Azhar Sheikh Ahmad tayyib ya gana da su, kuma ta roke shi da a kafa doka a kasar Masar wadda za ta haramta cutar da masu larura ta musamman a kasar ko kuma yi musu izgili saboda larurarsu.
Mahaifin Neda ya bayyana cewa, duk da cewa diyar sa ba ta je makarantar boko ba, amma ta iya magana da harshen turancin Ingilishi, kuma ta iya mu’amala da shafukan yanar gizo da kafofin sada zumunta.