Wata Balasdiniya Ta yi Shahada Sakamakon Bude Mata Wuta Da Sojojin Isra’ila Suka Yi.
Sojojin Isra’ila sun harbe wata bafalasdiniya a kuda da garin Baith laham dake kudancin gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, adaidai lokacin da rikici ke kara yaduwa a yankunan falasdinawa da aka mamaye.
Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar cewa sojojin Isra’la sun bude wuta kan wata mata mai suna Ghada Ibrahim alokcin da take kokarin ketara wurin binciken ababen hawa na soji a kusa da kauyen Husan wake yammacin baithlaham.
Matar yar shekaru 40 da haihuwa ta mutu ne a Asibiti a bait jala dake gabar yammacin kogin Jodan inda aka kaita domin yimata magani bayan da tayi ta zubar da jinni sakamakon harbin da aka yi mata.
READ MORE : Pakistan; Miliyoyin Mutane Na Zanga-Zangar Adawa Da Tsige Imran Khan.
Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin Isra’ila suka kara tsaurara mataken tsaro a yankunan falasdinawa bayan harin da wani bafalasdine ya kai a birnin tel Aviv a baya bayan anan da yayi sanadiyar halakar yahudawa 2 da kuma jikkata wasu 15.
READ MORE : Faransa; Macron Da Le Pen Za Su Je Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasa.
READ MORE : Iran; Dole Ne Amurka Ta Ba Da Tabbaci Daga Majalisa Kan Yarjejeniyar Nukiliya.