Wasu Sojojin Isra’ila Biyu Sun Jikkata Bayan Kai Musu Harin Ramuwar Gayya.
wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa wani harin ramuwar gayya da aka kai kan jmai’an yan sanda da na sojin gwamnatin haramtacciyar Kasar Isra’ila ya jikkata sojoji guda biyu a kauyen Silat Al-Harithiya dake yankin falasdinu a kusa da birnin Jenin dakae gabar yamma da kogin Jodan
majaliyar labaran yankin falasdinu sun nuna cewa wannan harin ya zo ne ‘yan sao’I bayan hari da wuka da aka kai kan sojojin Isra’ila a tsohon garin Birnin Qudus.
Sai dai an cafke Matukin motar day a kai harin ramuwar gayya da ya kai ga lalata motoci masu silke na sojojin Israila kuma ana ci gaba da yi masa tambayoyi a ofishin sojojin na Isra’la, tuni aka kai sojojin guda biyu da suka jikkata Asibiti domin yi musu Magana.
Wanna harin ramuwa gayyar yazo ne bayan da sojojin Israila suka harbe wani matashi bafalasdine a tsohon garin nan birnin Qudus bayan bullar rikici a birnin, gwamnatin telaviv tana shirin kwashe dukkan falasdinawa dake wajen , da kuma kai hari da gangan kan wani bafalasdine a lokacin yana sallah a harabar masallacin Qudus.