A lokacin ad suka kai ziyara a garin Aswan na kasar Masar, sun bayyana cewa, sun muslunta ne don kashin kansu ba tare da wani ya tilasta su ba.
Suka kyawawan dabiu irin na musulmi na burge su matuka a Burtaniya da ma kasashen turai da dama da suka je, musamman ma Muhammad Salah wanda shararren dan kwallo ne kuma yana rayuwa a garin Liverpool wanda shi ne garin iyayensu da kakanninsu.
Suka ce Muhammad Salah mutum mai kaskantar da kansa duk da irin sunan da ya yi a duniya da kuma kudi da yake da su, amma baya yin girman kai da izgili ga mutane, daga baya sai suka lura da cewa saboda shi musulmi ne, yana yin hakan ne bisa koyarwar addininsa, wannan ya yi musu tasiri har suka musulunta.
A wani labarin na daban zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna, babban sakataren cibiyar Ilimi ta Rasulul A’azam da ke birnin Kano a Najeriya, Sheikh Saleh Muhammad Sani ya bayyana cewa, ko shakka babu a kan cewa, yunkurin Imam Hussain (AS) ya zo ne domin tabbatar da sahihin tafarki na manzon Allah (SAW) tare da shata layi na bambance wannan sahihiyar hanya ta manzo daga sauran hanyoyi.
Malmin ya ce, Imam Hussain (AS) bai fito da domin neman fada da wasu ko neman dukiya ko matsayi ko wata daukaka ta duniya ba, ya fito ne domin samun inda zai samu natsuwa wajen yada addinin Allah ga bayinsa bisa sahihiyar koyarwa ta ma’aiki (SAW) wadda ba a gurbata ta ba.
A kan haka ne ma ya fito tare da iyalansa da wasu daga cikin sahabbansa da kuma zuriyar manzon Allah (SAW) wadanda suke tare da shi, wanda hakan yake kara tabbatar da cewa, lallai shi bai fito domin yaki ba.
Kuma wannan yana daga cikin kalamansa bayan da rundunar makiya ta tsare shi a Karbala, inda yake tabbatar musu da cewa, bai fito domin wani mugun nufi ko jabberanci ko barna ko zalunci ba, ya fito ne kawai domin samun damar yin gyara lamarin al’ummar kakansa da kuma kare addinin Allah madaukakin sarki.
A kan haka wannan zai kara tabbatar da cewa, Imam Hussain (AS) ya yi abin da yake ci gaba ne na tafarkin kakansa manzon (SAW) da kuma mahaifinsa Imam Ali (AS) da kuma dan uwansa Imam Hasan (AS) wanda kuma a lokacin ne shi ne jagoran Ahlul bait na manzon Allah a bayan kasa, shi ne mai wakiltar manzon Allah da alayensa da kuma al’ummar masu bin tafarkin manzon Allah.