Wasu Kungiyoyi A Sudan Sun Ki Halattar Zaman Sulhuntawa.
Rashin halartar kungiyoyi fararen hula masu tasiri a Sudan, zaman tattaunawan neman hadin kan kasar ya sanya an dage zaman tattaunawan karo na biyu da aka shirya gudanarwa.
Kakakin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ya bayyana cewa: An dage gudanar da zaman tattaunawa kan makomar siyasar kasar Sudan karo na biyu zuwa wani lokaci nan gaba da ba a tantance ba, saboda rashin halartar manyan kungiyoyin fararen hulan kasar masu adawa da mulkin soji a Sudan musamman gamayyar rundunar ‘yanci da canji ta Forces of Freedom and Change.
READ MORE : Jakadan Rasha; Ya kamata Isra’ila ta daina munanan ayyukan da take yi wa Siriya.
Kakakin tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Fadiy Alkadi ya bayyana cewa: Ci gaba da gudanar da zaman tattaunawan wanda aka shirya yi a ranar Lahadi, an dage zaman bisa kudurin bangarori uku masu shiga tsakani a kasar wato Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar tarayyar Afirka da kuma kungiyar Bunkasa harkar tattalin arzikin kasashen yankin Gabashin Afirka ta IGAD.
READ MORE : FM Nigeria yayi kira da a hada kan musulmi akan takfiriyya.
READ MORE : Taiwan – Amurka Ta Gargadi China Kan Ayyukan Sojinta A Kusa Da Taiwan.