Wasu Kasashen Larabawa Sun Yi Kira Ga HKI Da Ta Kiyaye Hurumin Masallacin Quds.
A bayani bayan taron da aka fitar na ganawa da aka yi tsakanin shugaban kasar Masar Albdul fatah Al’sisi da na Jodan Sarki Abdallah da sarkin Dubai shaikh Mohammad bin Zayed Al Nahyan an bukaci a kai zuciya nesa a rikin da ya barke tsakanin Falasdinawa da HKi , kana sun yi kira ga Isra’ila da kiyaye hurumin masallacin Quds mai tsarki.
Haka zalika sun yi kira ga Israila da ta dakatar da abin da suka kira wofantar da shirin samar da mafita kan rikicin na kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, kuma ta gaggauta samar da hanyoyi koma teburin shawrwari da Falasdinawa da gaggawa.
Wannan yana zuwa ne bayan da sojojin Israila suka kusta kai cikin masallacin Quds tare da yin amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu ibada,da hakan ya kai ha jikkata falasdinawa fiye da 200,, tuni fira ministan Isra’ila Naftali Bennett yayi wasu da batun koma teburin tattauna da kuma bawa falasdinwa yancin cin gashin kai.
Anasa bangaren sakatare janar din mdd Antonio Gutteres ya tattauna ta wayar tarho da fira ministan Isra’ila da shugaban Falasdinawa a kokari da yake yi na dakatar da rikicin da kawo karshe duk wani mataki da ka iya ruruta wutar rikicin.
Kana ya bukaci Isra’il da ta kiyaye hurumin masallacin Quds da dukkan mabiya addinai ke girmamawa.