Wasu jiga-jigan NNPP da dama sun koma APC a jihar Zamfara.
Wasu shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar NNPP daga kananan hukumomin jihar Zamfara goma sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Sun dai yi zargin cewa jaga-jigan uwar jam’iyyar ne suke musu kama-karya har ta kai ga jam’iyyar ta rasa dan takarar gwamnan da jama’a ke goyon baya, don haka ne suka gwammace su fice daga jam’iyyar.
Amma shugabannin NNPP a matakin tarayyar sun musanta wannan zargin suna cewa sayen su aka yi.
Shugabannin jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmarin sun bayyana cewa da shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar na kananan hukumomi 10 daga cikin kananan hukumomi 14 da ke jihar ne da ƙwansu da kwarkwata suka yi hijira daga NNPP zuwa APC mai mulki sakamakon zargin kama-karya da suka ce ana yi musu.
A cewarsu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu sun yi babakere a jam’iyyar sun hana kowa sakat.
Hon Babangida Haruna Damba shi ne tshon sakataren tsare-tsare na jam’iyyar NNPP a jihar Zamfara da suka jagoranci wannan hijira.
Sai dai shugabannin jam’iyyar NNPP a matakin tarayyar sun musanta wannan zargin suna cewa sayen masu sauya shekar aka yi, kuma tafiyarsu ba za rage wa NNPP komai ba.
Injiniya Buba Galadima na cikin wadanda ake zargi da takura shugabannin jam’iyyar, wanda ya ce NNPP na da ɗan takarar gwamna a jihar Zamfara.
Mako uku kenan da zuwan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Injniya Rabiu Musa Kwankwaso jihar Zamfara, inda rahotanni ke cewa ya zauna da shugabannin jam’iyyar domin ya ji koke-kokensu da nufin share musu hawaye.
Amma sai ga shi kwatsam wadannan shugabanni da magoya bayansu sun sanar da ƙaurar da rikiɗar da suka yi daga NNPP zuwa APC.
Kuma duk da jaga-jigan jam’iyyar na cewa Allah raka taki gona, masu sharhi a kan harkokin siyasa na cewa hakan babban koma-baya ne!