Firayi ministar kasar New Zealand ta bayyana cewa, mutumin dan kasar Sri Lanka ne, kuma ya kwashe tsawon shekaru 10 yana zaune a kasar ta New Zealand, sannan kuma tun shekaru 5 da suka gabata ne jami’an tsaro suke sanya ido a kansa saboda take-takensa.
Ta ce mutumin ya tasirantu da ra’ayoyi na tsatsauran ra’ayi irin an ‘yan ta’addan Daesh, wanda hakan yasa ake kallonsa a matsayin wanda zai iya aikata ta’addanci a kowane lokaci, kuam hakan ta faru.
Firayi ministar ta ce daga lokacin da ya kai harin an kashe kasa da minti daya, duk kuwa da cewa dai ya raunata mutane ta hanyar daba musu wuka.
Jami’an tsaro sun ce ya shiga babban shagon New Lynn ne, inda ya fara daba wa mutane wuka, ya kuma jikkata mutane 6, kuma 3 daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
A wani labarin na daban majiyoyin kungiyar Taliban sun kungiyar ta kammala kwace iko da jihar Panjshir a kasar Afhanistan, bayan dauki ba dadi da mayakan kungiyar suka yi da magoya bayan Ahmad Mas’ud, wanda yaki mika kai ga kungiyar.
A cikin wani bayani da kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya yi ga mayakan kungiyar a cikin filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul, ya bayyana cewa, an kawo karshen yaki a kasar, kuma sun shimfida ikonsu a jihar Panjshir wadda taki mika wuya.
Baya ga haka kuma kungiyar ta nuna hotunan bidiyo na babban ginin gwamnatin jihar Panjshir, inda mayakan kungiyar suka saukar da tutar kasar Afghanistan da ke wurin, suka dora tutarsu.
Sai dai a nasa bangaren Ahmad Mas’ud wanda ke jagorantar mayakan yankin na Panjshir wajen yin turjiya a gaban mayakan Taliban tare da kin mika wuya gare su ya karyata cewa Taliban ta kammala kwace iko da jihar baki daya.
Haka nan kuma ya yi ikirarin cewa, sunan nan cikin jihar kuma za su gaba da yaki da Taliban, kamar yadda ya bukaci al’ummar Afghanistan da su mike su kwaci ‘yancin kansu daga mulkin mallakar Taliban.