Wannan wani bawan Allah ne wanda ke hidima ga masu ziyarar arba’in ta Imam Hussaini (S.a), kuma cikin nishadi da walwala kai zakayi tsammanin ba abinda yake tattare dashi na tawaya.
Tattakin arba’in na Imam Hussain (S.a) dai an saba gudanar dashi duk shekara, inda ake takawa daga najaf zuwa karbala a kafa domin nuna kuna gami ga biyayya ga jikan manzon Allah (S.a.w.w).
Rahotanni daga kasar Iraki dai na tabbatar da cewa a tunishirye shirye suka kankama domin gudanar da wannan ibada mai dinbin tarihi.
Wani maniyyaci da muka tattauna dashi ya tabbatar mana da cewa bana ma an shirya gudanar da wannan tattakin amma an saka matakan kula da lafiya gami da tabbatar da tsaro a wajen tattakin na bana.
Ga wanda ya taba zuwa wannan ziyarar zai tabbatar da yadda ‘yan uwa musulmi mazauna Iraki ke dawainiya da mutane, kama daga lamarin masauki, abinci, abin sha kula da lafiya da dai sauran su, wasu bayin Allah sun sadaukar suna ta yima maziyarta hidima.
Daga kasashe daban daban kama daga Asiya, nahiyar turai dama nahiyar afirka ake kwararowa zuwa wannan babbar ibada mai dimbin tarihi gami da lada.
Abu mafi muhimmanci yadda ake nuna ‘yan uwantaka a wannan kwanaki da aka hadu domin gudanar da ibadar ta tattaki.
Wani abin sha’awa kusan kowanne bangaren akida da addinai sukan yi musharaka a wannan ibada kama daga ‘yan shi’a ahlussunnah kai har ma da kiristoci sukan shiga ayi wannan tattaki dasu.
Idan kana wannan tafiya baza ka taba kukan rashin wani abu ba domin hatta takalman ka a kwai matasa wadanda suka sadaukar suna gyara gami da wanke takalman mutane, ga kuma bangaren masu lura da lafiyar mutane, masu raba shayi da abinci dama bangaren masu yima kafafun mutane tausa idan sun yada zango.
Bincike ya tabbatar da cewa tafiya mafi nisa da ake tattakawa itace daga khurasan watau mashhad ta kasar Iran zuwa karbala ta kasar Iraki.