Wani Bapalasdine Ya Yi Shahada A Kusa Da Birnin Quds A Yau Lahadi.
Bapalasdinen matashi ya yi shahada ne sanadiyyar harbinsa da sojojin mamaya su ka yi a kusa da Babul-Hiddha da ke arewacin masallacin Quds , bisa zargin cewa ya kai wa ‘yan sandan mamaya biyu hari da wuka.
Saurayin mai suna Jamal al-Kawasimy dan shekaru 19 wanda ya fito daga garin al-Dhur, ya fadi kwance cikin jinni har rayi, ya yi halinsa.
Majiyar ‘yan sahayoniya ta “Why Net” ta ambaci cewa; ‘Yan sandan sahayoniya biyu sun jikkata sanadiyyar harin da Bapalasdine din ya kai musu.
A gefe daya, kungiyoyin gwagwarmayar palasdinawan sun jinjinawa saurin Bapalasdinen saboda harin da ya kai wa ‘yan sandan mamayar biyu da jikkata su.
Kungiyar Jihadul-Islami ya bayyana cewa; Shahadar da bapalasdinen a kusa da masallacin Quds, wani Karin yunkuri ne ba kare masallacin mai albarka daga najasar ‘yan sahayoniya.
Ita ma kungiyar gwgawarmaya ta Hamas ta yabawa Bapalasdinen tare da jinjina masa akan jaruntarsa ta kai wa ‘yan sahayoniyar hari.