Wani Bafalastine Dauke Da Bindiga Ya Raunata Yahudawa 9 A Birnin Quds.
Rahotanni daga Isra’ila na cewa mutum akalla tara ne suna jikkata, yayin da wani bafalastine dauke da bindiga ya bude wuta kan wata motar safa a tsakiyar birnin Quds.
Bayanai sun ce ‘yan sandan Isra’ila na ci gaba da farautar maharin da ya tsare, a yayin da jami’an agaji suka ce mutum bakwai sun jikkata ciki har da biyu da suka ji munannen rauni.
Kafafen yada labaran Isra’ila sun rawaito cewa an kai hare-hare guda biyu a wasu unguwanni biyu na birnin al-Quds da Isra’ilar ta mamaye.
Kamfanin dillancin labaran Isra’ila ya bayyana cewa, mutumin ya yi harbin bindiga 10 a cikin dakika 10-15, inda ya nufi wata motar bas da motoci biyu sannan ya fice daga wurin.
Majiyoyin Falasdinawa sun ce jami’an tsaron Isra’ila masu yawa sun kutsa cikin unguwar Silwan da ke birnin, inda suke neman maharin.
Sun kuma kara da cewa jiragen Isra’ilan sun kuma yi ta shawagi a unguwar Silwan domin neman maharin, wanda har yanzu ba a kama shi ba.
Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta mayar da martani kan harin na Quds, inda ta bayyana hakan a matsayin wani martani na Falasdinawa kan hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila suke yi da kuma laifukan da suke aikatawa a kullum a kan al’ummarsu, da kasarmu, da wurarensu masu tsarki.