Wasa na cikin abubuwan da suke taimakon yara wajen inganta lafiya da walwalar su.
Amma duk da cewa MDD ta ce duk yara suna da hakkin yin wasa, miliyoyi a yankunan da ake yaki ba su samu damar ba – kamar a Falasdinu da Myanmar da Sudan da Congo.
A Gaza, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa sama da yara 15,00 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta fara hare-harenta a kasar a ranar 8 ga Oktoban 2023.
Yadda duniyar take kara fuskantar yake-yake, kananan yara ne suka fara fuskantar matsalolin da hakan ke zuwa da shi, inda sukan sha fama da damuwa rashin walwalar da raunuka a sanadiyar yake-yaken da babu ruwansu.
Watakila ranar 11 ga Yuni, wadda ranar ce Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana da Ranar Wasanni ta Duniya, ita ma ta zama tamkar sauran ranaku irinta domin tuna rayuwar miliyoyin yara da suka makale a kasashen duniya da ake yaki irin su Falasdinu da Sudan da Dimokuradiyyar Jamhuriyar Congo da Ukraine da Myanmar.
Babban Daraktan Asusun UNICEF, Catherine Russel, ta ce an ware ranar ce domin yara su fahimci cewa, “za su iya gudanar da rayuwarsu komai wahalar da suka tsinci kansu a ciki.”
Kididdiga ta nuna girman lamarin. Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya a kan kuncin da yara suke rayuwa a ciki a garuruwan da ake yaki ya nuna yadda suka fuskanci matsananciyar damuwa a shekarar 2023, inda aka samu mace-macen yara da dama, wasu suka jikkata a yankunan Falasdinu da Sudan da Myanmar.
Kungiyoyin Ba da Agajin Gaggawa sun ruwaito yadda yara da dama suka mutu a yake-yaken da babu hannunsu a ciki. Wadanda kuma suka tsira, suna rayuwa ce ta kunci da damuwa da ba za su taba mantawa da ita ba har abada.
Alamun yaki – Yaran da suka samu raunuka a Gaza
Yaran da aka kama cikin rikici suna da tabo ta jiki da ta hankali wanda zai iya azabtar da su har tsawon rayuwarsu. Hoto: Getty Images
A Gaza, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa sama da yara 15,00 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta fara hare-harenta a kasar a ranar 8 ga Oktoban 2023.
Wakiliyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a kan harkokin yara da yake-yake, Virginia Gamba ta ce sun saka jan fenti a kan sojin Isra’ila bisa samunsu da laifin kashe dalibai ‘yan makaranta da marasa lafiya a asibitoci.
Bayan barazanar harin bama-bamai da suke fuskanta, fararen hula a Gaza suna kuma fama da rashin ababen bukata irin su ruwan sha da na girki da wanki da sauransu.
Yanzu haka sama da yara 3,500 da suka tsira da ransu, amma suke fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki.
A Sudan kuma, an kashe kusan yara 500, sannan sama da 700 sun samu raunuka duk da an tsagaita wuta tsakanin sojojin Sudan da jami’an tsaron Rapid Support Forces masu tada kayar baya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai hari a makarantu da asibitoci guda 85 tun farkon fara yakin a Khartoum a ranar 15 ga Afrilun 2023.
Asusun UNICEF ya sa Sudan a cikin daya daga cikin kasashen da suke da matukar wahalar rayuwa ga yara. Wani rahoto ya nuna cewa akalla yara miliyan 19 ne suke fuskantar barazanar daina zuwa makaranta, wanda hakan zai shafi ci gaban rayuwarsu.
DUBA NAN: Zafi Yayi Sanadin Mutuwar Fiye Da 900 A Hajjin Bana
Makarantu da dama a Sudan sun zama matsugunin ‘yan gudun hijira akalla miliyan 8.