Cibiyar da ke sa idanu kan lamurran da suka shafi wasanni ciki har da ilimin da yi wa wasannin da’ira, CIES, ta bayyana dan wasan gaba na Real Madrid Vinicius Junior a matsayin dan kwallon ya fi daraja a duniyar tamaula.
A halin yanzu dai an kiyasta cewa darajar Vinicius mai shekaru 21 dan kasar Brazil kan euro miliyan 166, inda ya doke Phil Foden na Manchester City, da Erling Haaland na Burossia Dortmund wajen zama akan matsayi na daya.
A kakar wasa ta bana, gudummawar cin kwallaye 12 da kuma taimakawa wajen jefa wasu 9 Vinicius ya ba da a cikin wasanni 25 da ya bugawa Real Madrid a gasar La Liga da ta cin kofin Zakarun nahiyar Turai.
A wani labarin nna daban Dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema ya taka rawa wajen cin kwallaye 4 daga cikin 6 da kungiyar ta sa ta lallasa Mallorca da su, yayin karawar da aka tashi 6-1 a daren ranar Laraba.
Yayin karawar da Mallorca ne kuma dan wasan na Faransa ya ci wa kungiyarsa kwallo ta 200, bayan kammala hutun rabin lokaci.
To shi ma dai Marco Asensio ya nuna bajinta yayin karawar da suka lallasa tsohuwar kungiyar ta sa Mallorca da kwallayen 6 inda ya ci 3 daga ciki.
A halin yanzu Real Madrid ta sha gaban Atletico Madrid a saman teburin La Liga da nasarar da ta samu da maki 16, yayin da Atleticon ke da 14.